Buhari Ya Roki Kasashen Duniya Su Yafe Basussukan Da Suke Bin Najeriya

Rahotanni dake shigo mana daga zauren Majalisar ?inkin Duniya dake birnin New York na ?asar Amurka na bayyana cewar mai girma Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma’a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya da su yafewa kasashe masu tasowa bashin da suke binsu.

Haka kuma, shugaban ya taya Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres murna zabensa da aka yi a matsayin babban sakataren majalisar tare da nuna godiya ta nada Hajiya Amina Mohammed daga Najeriya a matsayin mataimakiyar Sakataren majalisar dinkin duniya a karo na biyu.

Rokon na Shugaban kasar na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ta shiga jerin kasashen duniya da bashi ya yi wa kanta.

Related posts

Leave a Comment