Sakamakon Bincike: Ministan Shari’a Na Duba Yiwuwar Mika Abba Kyari Amurka

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sifeta Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya tuhumi tsohon kwamandan rundunar IRT, Abba Kyari, kan alakar da aka gano ya na da ita da Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi, gagarumin dan damfarar yanar gizo.

An ruwaito cewa, ofishin antoni janar na tarayya na bukatar a duba bukatar da Amurka ta turo na bada fitaccen dan sandan domin gudanar da bincike a kanshi.

An mika tuhumar ne bayan binciken da wani kwamitin bincike ya yi, wanda ya bankado al’amuran da ke faruwa. Wata kotun Amurka ta na tuhumar Kyari da hada kai tare da karbar $1.1 miliyan kan wata damfara da Hushpuppi yayi wa wani dan kasuwar Qatar.

Hukumar kula da lamurran ‘yan sanda ta dakatar da Kyari daga matsayinsa na mataimakin kwamishinan ‘yan sanda kuma shugaban rundunar ta musamman ta IRT sakamakon bukatar da Alkali ya mika.

An gano cewa, kwamitin bincike da ya samu shugabancin DIG Joseph Egbunike, wanda ya mika rahoton bincikensa a watan Augusta, ya tabbatar da cewa an samu sadarwa tsakanin Kyari da dan damfarar.

Kwamitin ya gano cewa an samu sadarwa tsakanin Kyari da Hushpuppi wanda ya yi karantsaye ga aikin dan sanda,” wata majiya babba ta tsaro ta sanar da hakan.

Sai dai, kwamitin bai bada shawarar a mika Kyari ga Amurka ba saboda ba a ga wani laifi da fitaccen dan sandan yayi wa Amurka ba. “Babu wata shaida da ke nuna cewa akwai laifin da dan sanda yayi wa Amurka da ya dace a mika shi kasar.

Hukumomin da suka dace ne za su ladabtar da shi. “Sai dai kuma, Ministan Shari’a zai bada shawarar ko za a mika shi Amurka, wanda da wuya hakan ta faru,” ya kara da cewa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba a wata tattaunawa da yayi a waya, ya ce kamar yadda aikin ‘yan sanda ya ke, sifeta janar ya mika shawarar kwamitin binciken ga hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda domin daukan matakin da ya dace.

Related posts

Leave a Comment