Yau Juma’a Ne Ake Daura Auren Yusuf Buhari Da Zahra Bayero

Rahotanni daga Fadar Shugaban Kasa na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhari, ya tura tawagar wakilai na musamman domin ?aura auren ?ansa, Yusuf da Zahra, ?iyar sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero, wanda za’a gudanar a yau juma’a a garin Bichi fadar Masarautar Bichi dake Jihar Kano.

Tawagar wakilan, bisa jagorancin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ?asa, Farfesa Ibrahim Gambari, zata je Kano ne domin halartar ?aura auren da aka shirya gudanarwa ranar yau Jumu’a.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai taken, “Tawagar shugaban ?asa zuwa Kano domin halartar manyan taruka biyu.”

Kakakin shugaban ?asa, Malam Garba Shehu, shine ya fitar da wannan sanarwa ranar Alhamis. Shugaba Buhari Ya Tura Wakilai Na Musamman Zuwa Kano Domin Daura Auren Yusuf da Gimbiya Zahra.

A cewar sanarwar, tawagar fadar shugaban ?asan sun ha?a da ministoci kamar ministan tsaro, Bashir Salihu Magashi. Sannan akwai ministan noma, Alhaji Sabo Nanono, Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, da kuma ministan albarkatun ruwa, Hussein Adamu.

Sai dai bayan kammala ?aura auren, Mallam Garba Shehu zai tsaya ya wakilci shugaba Buhari a wurin taron mika sandar mulki ga sarkin Bichi.

An tsaurara tsaro a Bichi Masarautar Bichi a jihar ?ano ta cika da jami’an tsaro ta ko ina yayin da ake cigaba da shirye-shiryen ?aura auren Yusuf, ?a namiji ?aya tilo ga shugaban ?asa Muhammadu Buhari , da amaryarsa Zahra, ?iyar sarkin Bichi.

READ ALSO Gwamnoni, Attajirai, da sauran manyan kasa za su je Bichi wajen auren ‘Dan Shugaban kasa Shirye-shirye sun yi nisa domin ?aura auren wanda aka tsara za’a gudanar a babban masallacin Jumu’a na Bichi da karfe 1:30 na ranar yau Jumu’a.

Related posts

Leave a Comment