Saudiyya Na Sahun Gaba Wajen Bada Agaji A Duniya – Rahoto

Rahotanni daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya na bayyana cewar ?asar ce ta uku a duniya kuma ta farko a ?asashen larabawa wajen bada taimakon jin-kai ga ?asashe marasa karfi a duniya.

Tallafin da take bayarwa ya haura dala miliyan 841, sannan masarautar ita ce babbar mai bada tallafi ga Yemen tare da gudunmawar da ta kai miliyan 800 a cewar binciken Majalisar Dinkin Duniya.

A lokacin da ya ke tsokaci, mai taimakawa sarkin Saudiyya kan harkokin agaji da jin-kai, Dr Abdullah Al-Rabeeah, ya ce sun kai ga wannan nasarar ne sakamakon goyon bayan da gudumawa da suke samu daga Sarki Salman da Yarima Muhammed Bin Salman.

Sannan ya shaida alfannun taimako karkashin shugabancin maarautar bisa koyarwa addini kan muhimmanci taimako musamman ga mabukata a ko ina a fadin duniya.

Related posts

Leave a Comment