Mai Alfarma Sarkin Musulmai, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana cewar ?asa Najeriya ta kaucewa hanyar da aka santa a kai, inda ya ce matsalar karancin abinci na haifar da ?arin matsalar rashin tsaro a Najeriya da rashin sanin inda aka fuskanta.
Sarkin Musulmin, ya bayyana cewa yunwa ba ta da hankali, bisa ga haka ina kara kira ga shugabanni a dukkanin matakai da su taimaka su kai wa jama’ar su ?auki domin yaki da matsalar yunwa.
Mai alfarman ya bayyana hakane a ranar Alhamis a jihar Gombe bayan ya hallarci wajen taron koli na neman zaman lafiyar kasa, wanda majalisar Da’awah ta Najeriya ta shirya.
Matsalolin Najeriya na cigaba da karuwa a kowacce rana, kada mu dinga yaudarar kan mu cewa abubuwa na gyaruwa, babu wani cigaba da ake samu.
Abinda muka rasa a kasar nan gaskiya, saboda babu wani addini da ya bukaci wani ya kashe wani.
Matsaloli na ta’addanci, ‘yan fashi, da masu garkuwa da mutane na cigaba da kawo cikas a harkar kasuwancin kasar nan.
