Gamayyar kungiyoyin cigaban yankin Arewacin Najeriya Jihohi 19 har da Abuja, sun fito fili sun goyi bayan maganar da tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida ya yi na kiran a haramtawa tsofaffi yin takarar shugabancin kasa.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Kaduna, Shugaban gamayyar kungiyoyin, Alhaji Nastura Ashir Shereef, ya bayyana kalaman tsohon Shugaban a matsayin abin a yaba, kuma wadanda suka zo a lokacin da ake da bukatar su.
Ashir Shereef ya kara da cewar tun farko su a matsayin gamayyar kungiyoyin Arewa sun taba kira akan wannan matsala da cewar a hana tsofaffi yin takarar shugabancin kasa, a bar Matasa masu jini a jika su yi takara, domin abubuwa sun sauya.
Gamayyar kungiyoyin sun bayyana cewar babban abin da ya jefa Najeriya halin da ta tsinci kanta yanzu a ciki shine tsofaffi dake jan ragamar mulkin kasa, inda suka bada misali da shugaba Buhari wanda tsufa ta sa mulkin shi ya zama jeka na yi ka.
Dangane da wata magana da gwamnan jihar Kaduna El Rufa’i ya yi a kwanakin baya na cewar ya yi wa Najeriya tsufa a matsayin shugaba, Ashir Shereef ya ce maganar El Rufa’i borin kunya ne domin ya sani cewar babu wanda zai za?e shi saboda irin mugun mulkin da ya yi a kaduna.
“kamar abin nan ne da aka ce da makaho ga ido yace suna wari”.
Gamayyar kungiyoyin sun bayyana yakinin su akan cewa matasan masu jini a jika sune za su kai kasar gaba, har an cimma bukatun da ake nema.
