Najeriya Ta Yi Cigaba Irin Na Mai Hakar Rijiya – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Mohammed Sa’ad Abubakar III, ya ce abubuwa suna kara tabarbare wa a Najeriya, ana fama da karancin abinci, lamarin da a har kullum yake ?ara mayar da Najeriya baya.

Sarkin Musulmi ya kara da cewa yunwa ta addabi ‘yan Najeriya, ga fatara da rashin tsaro, babu wanda yake cikin hayyacin shi, dole a tausaya mana.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi magana ne a kan hadin-kai a Najeriya a wajen wani taro da majalisar Da’wah Coordination Council of Nigeria ta shirya a Gombe.

“Abin da mu ka rasa a kasar nan shi ne gaskiya da fada wa kanmu gaskiya wajen yin abin da zai fishe mu, domin babu addinin da ya ce a kashe mutum.”

“Ta’addanci, tada zaune-tsaye da garkuwa da mutane su na ci, kuma masu wannan aiki suna yawo abinsu.” “Mutane da yawa suna cikin yunwa, domin ba za su iya sayen abinci ba; farashi ya na kara tashi sama kullum.

A tabbatar akwai abinci saboda talaka ya samu.” “Idan babu abinci, babu zaman lafiya, idan babu zaman lafiya, babu tsaro, idan babu tsaro, babu cigaba, idan babu cigaba, za mu rika rayuwa ne haka kurum.”

Related posts

Leave a Comment