Rundunar Yansandan Jihar Katsina, ta samu nasarar chafke wata mata mai suna Aisha Nura mai Shekaru 27, yar Kauyen Baranda dake a karamar Hukumar Batsari kuma matar Kasurgumin Dan Bindiga Nura Alhaji Murnai, dauke da kudi sama da naira miliyan 2 da Dubu Dari hudu.
Acewar Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya bayyana, an chafke matar ne bayan samun rohoton sirri daga bakin yan kasa na gari, a dai-dai lokacinda take yunkurin hawan mashin na achaba kuma tanata boye kudin dake hannunta.
Kamar yadda ya shedawa manema labaru, ana zargin kudin na cinikin Makamai ne a tsakanin mijin nata da masu safarar makamai a Kaduna, lura da cewar yan ta’addan a halin yanzu sun chanza salon amfani da mata wurin safarar makamai.
Da take jawabi ga Yan Jarida, Matar Dan ta’addan Aisha Nura tace mijinta Nura Alhaji Murnai shine ya aiketa a Kaduna domin ta karbo mashi kudaden daga hannun wani.
A sabili da haka a halinda ake ciki akwai bukatar jami’an tsaro su kara sa ido, domin yan ta’adda suna amfani da mata wurin safarar makamai da kayayyakin amfaninsu na yau da kullum a halin yanzu.
