Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar duk da majalisar dattawa ta yi fatali da rokon shugaban kasa na nada Lauretta Onochie a matsayin kwamishinar INEC, watakila a sake aika sunanta domin tantancewa a karo na biyu.
A ranar Talata, 13 ga watan Yuli, 2021, ta ce wata majiya dake fadar shugaban kasa ta shaida cewa za a kuma tura sunan Onochie. Majiyar ta ce har gobe shugaban kasa bai fitar da rai cewa Misis Onochie za ta hau kujerar babbar kwamishina na hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ba.
Rahotanni sun bayyana cewar har zuwa yanzu, shugaba Muhammadu Buhari bai janye sunan hadimar ta sa daga majalisar tarayya ba, hakan ya nuna sam bai karaya da ita ba.
“Ganin cewa har yanzu mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya bada sunanta bai janye ba, ya nuna ya yarda da tsarin da ake bi.” “Sannan ya yarda cewa za a iya tantance Onochie (Lauretta).
Zuwa yanzu fadar shugaban kasa ba ta ce komai ba a kan matakin da Majalisar ta dauka. An tuntubi Mallam Garba Shehu domin jin ta bakinsa, amma hakan bai yi nasara ba. Bai amsa kiran da aka yi masa a waya ba, sannan bai tanka sakonni ba.
Hujjar da kwamitin da ya zauna da wannan mata ya bada shi ne nada ta a kujerar kwamishina zai ci karo da tsarin FCC da ta ce a ba kowace jiha dama iri daya. Kafin a sake kai wa majalisar dattawan kasar sunan Onochie, ya kamata kwamishina mai-ci a yanzu da ta fito daga jihar Delta ta yi murabus, ta ba hadimar dama.
