Buhari Ya Yi Tir Da Harin Da Boko Haram Ta Kai Jihar Adamawa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa, Muhammadu Buhar ya yi tir gami da Allah wadai bisa kisan gilla Boko Haram suka yi wa wasu yan Najeriya da suka ha?a da wani shugaban yan tawagar bijilanti da dagacin ?auyen Dabna dake ?aramar hukumar Hong, jihar Adamawa.

Da yake martani kan lamarin, shugaba Buhari yace “Wannan ta’asar, rashin imani, da rashin mutunci ne kuma ?aukar rayuwar mutane ba zai tafi hakanan ba.

A wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis, Buhari ya umarci jami’an tsaro cewa “ku ninka ?o?arin da kukeyi wajen ?aukar mataki a kan wannan barazanar tsaron cikin gaggawa.”

“Ba zamu amince mu baiwa yan Najeriya kunya ba dangane da amanar da suka dan?a a hannun mu na tsare rayuwarsu.” inji shi.

Gwamnati zata tallafawa iyalan wa?anda abun ya shafa, Shugaba Buhari ya umarci hukumomin da abun ya shafa ?ar?ashin jagorancin ma’aikatar jin ?ai da walwala da su gaggauta gano abubuwan da aka rasa a wa?annan yankuna kuma su tura da tallafin gwamnati.

Related posts

Leave a Comment