Borno: Harbin Bindiga Muke Koyarwa Ba Ta’addanci Ba – Kungiyar Faransa

Kungiyar agaji ta Faransa da gwamnatin Borno ta dakatar da ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya ta ce babu wani ma’aikacinta da ke dauke da bindiga.

A ranar Asabar ne Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya sanar da dakatar da ayyukan ?ungiyar bayan mazauna kusa da wata otal a garin Maiduguri sun bayar da rahoton jin ?arar harbin bindiga.

Hukumomin Borno sun zargi ?ungiyar da koya wa mutane harbin bindiga.

Amma Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ce a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Lahadi, Acted ta ce tana ?o?arin tabbatar da tsaron ma’aikatanta ne a yankin da ke fama da matsalar Boko Haram tsawon shekara 12 “ta hanyar horo da atisaye.”

?ungiyar ta bayyana atisayena matsayin “tsari na ?ungiyoyi da ke aiki a Najeriya da sauran ?asashe, kuma ma’aikata ba su yawo da bindiga da kuma wurin da ake atisayen,” in ji sanarwar.Article share tools

Related posts

Leave a Comment