Kungiyar agaji ta Faransa da gwamnatin Borno ta dakatar da ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya ta ce babu wani ma’aikacinta da ke dauke da bindiga.
A ranar Asabar ne Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya sanar da dakatar da ayyukan ?ungiyar bayan mazauna kusa da wata otal a garin Maiduguri sun bayar da rahoton jin ?arar harbin bindiga.
Hukumomin Borno sun zargi ?ungiyar da koya wa mutane harbin bindiga.
Amma Kamfanin dillacin labaran Faransa ya ce a cikin sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Lahadi, Acted ta ce tana ?o?arin tabbatar da tsaron maaikatanta ne a yankin da ke fama da matsalar Boko Haram tsawon shekara 12 ta hanyar horo da atisaye.
?ungiyar ta bayyana atisayena matsayin tsari na ?ungiyoyi da ke aiki a Najeriya da sauran ?asashe, kuma maaikata ba su yawo da bindiga da kuma wurin da ake atisayen, in ji sanarwar.Article share tools

