?ungiyar masu bu?ata ta musamman reshen Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun sha alwashin kawo wa ?an takarar shugabancin ?asa ?ar?ashin Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ?uri’u dubu 25 a babban za?en dake tafe.
?ungiyar ta bayyana hakan ne a yayin wani gangami da ta shirya wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna ranar talata.
Da yake jawabi a yayin taron uban ?ungiyar na ?asa Sanata Hayatu Bello Gwarzo, ya bayyana cewar bayan tantancewar da suka yi wa dukkanin ‘yan takarar ne suka tabbatar babu wanda ya dace da zama shugaban ?asa sakamakon kyawawan manufofi da yake dasu kamar Wazirin na Adamawa Atiku Abubakar.
Anashi ?angaren jigon kungiyar na jihar Kaduna Abdullahi Bugun ya bayyana cewar ba su da wani ?an takara a za?en shugaban ?asa sai Atiku domin ya nuna musu cewar shi nasu ne.
Taron ya samu halartar ‘ya’yan ?ungiyar daga shiyyar Arewa maso yamma tare da alkawarin zabar jam’iyyar PDP daga sama har ?asa.
