Amfani Da Tsoffin Kudi Ya Haramta A Najeriya – Babban Banki

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu ruwan sa da umarni ko hukuncin da Kotun ?oli ta yanke a makon da ya gabata, ko wanda za ta yanke a ranar 15 Ga Fabrairu.

Ya ce duk wani mai ri?e da tsoffin ku?in Naira 200, 500 da kuma 1000, to ba shi da bambanci da mai kayan ?arangar takardar tsire, domin ba zai iya hada-hada da ku?in a yanzu ba.

Ya fa?i haka ne a ranar Talata, lokacin da ya kai ziyara Ma’aikatar Harkokin Waje, a Abuja.

A ranar 8 Ga Fabrairu Kotun ?oli ta ?ara kwana bakwai daga wa’adin 10 Ga Fabrairu wanda Emefiele ya ?ara lokacin da ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a Daura.

Sai dai kuma tun bayan da Kotun ?oli ta yi ?arin wa’adin, CBN ba ta yi magana ba, sai yau, jajibirin ranar ?arewar wa’adin, kafin a ji abin da Kotun ?oli za ta zartas kuma ranar Laraba, 15 Ga Fabrairu.

A ranar Litinin dai mafi yawan masu manya da ?ananan kasuwanci sun daina kar?ar tsoffin ku?a?e. Amma lamarin ya fi muni a ranar Talata.

A ranar Talata ?in ce kuma Emefiele ya bayyana cewa CBN ba zai ?ara ko kwana ?aya daga tsohon wa’adin da ya bayar ba.

“To ai yanzu lamarin ya yi sau?i sosai, tunda bankuna sun fara biyan mutane ku?a?e a kan kanta. Kuma masu POS su ma su na biyan ku?a?en.” Inji Emefiele.

“Saboda haka babu bu?atar a ?ara ko da wa’adin rana ?aya kuma daga 10 ga Fabrairu.”

Emefiele ya zargi wasu ‘yan siyasa da laifin ?oye sabbin ku?a?e.

“Wasu shugabannin mu su na sayen sabbin ku?a?e su na ?oyewa, su na kimshewa saboda wasu dalilai. Ba na son bayyana abin da za su yi da ku?in.” Inji Emefiele

Related posts

Leave a Comment