Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda ya yi gwamna a jihar Kano sau biyu ya yi wa manyan jamiyyun siyasar Najeriya watau PDP da APC wankin babban bargo bisa gazawarsu a mulki.
Madugun na Kwankwasiyya ya ce jamiyyun biyu duk ba su da abubuwan da za su nuna domin alummar kasar nan su zabe su a 2023.
Kwankwaso ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi hira da gidan rediyon Nasara FM ranar Lahadi 20 ga watan Fubrairu shekarar 2022.
A cewar Rabiu Musa Kwankwaso, jamiyyarsa ta PDP mai adawa da APC mai mulki, cike suke da yan siyasan da bai dace mutane su sake kada masu kuria ba. Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi kira ga alummar kasar nan su nemi jamiyyar da za ta fitar da su daga cikin halin da wadannan jamiyyu suka jefa kasar a ciki.
Ban ga abin da jamiyyar PDP ko APC za su nuna, ko su fadawa Yan Najeriya ba domin su gamsu, su zabe su a zabe mai zuwa na 2023 ba. Saboda haka ina tunani mutane su zauna, su yi tunanin jamiyya da mutanen da ya dace su zaba domin ceto su daga halin da aka shiga.

