2023: Buhari Ya Kalubalanci Jami’an Tsaro Da Zama ‘Yan Ba Ruwanmu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi kira ga hukumomin tsaron ?asar da za su yi aiki da hukumar za?en ?asar a lokacin za?ukan 2023 da ke tafe da su kasance ‘yan ba-ruwanmu, tare da nuna ?warewar aiki.

Sannan kuma su nesanta kansu daga duk abubuwan da za su kawo matsala ga ayyukansu.

Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga jami’an ne ranar Laraba a lokacin bikin ?addamar da rukunin gidajen jami’an hukumar tattara bayanan sirri a unguwar Idu da ke Abuja babban birnin ?asar.

Buhari ya umarci hukumomin tsaron da su tabbatar da cewa sun kula da ayyukan rarraba tare da lura da muhimman kayayyakin za?e cikin nuna ?warewar aiki kamar yadda yake kunshe cikin dokokin hukumomin tsaron.

Related posts

Leave a Comment