?etare: An Kawo ?arshen Mulkin Natanyahu A Isra’ila

Benjamin Netanyahu ya rasa ikonsa na shekaru 12 kan mulkin Isra’ila bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar amincewa da sabuwar gwamnatin ha?aka.

Naftali Bennett na jam’iyyar Yamina zai jagoranci sabuwar “gwamnatin ta canji.”

Shi zai jagoranci gamayyar jam’iyyun da suka samu rinjayen ?uri’a ?aya wanda ya kai ga kawo ?arshen mulkin Netanyahu.

Mr Bennett zai zama Firaminista har zuwa watan Satumban 2023 ?ar?ashin tsarin kar?a-kar?a.

Daga nan zai mi?a mulki ga Yair Lapid, shugaban jam’iyyar Yesh Atid, na tsawon shekara biyu.

Mista Netanyahu – wanda ya fi da?ewa kan mulki a Isra’ila ya mamaye siyasar Isra’ila na tsawon shekaru.

Yanzu zai kasance shugaban jam’iyyarsa ta Likud kuma jagoran adawa.

Lokacin da ake tafka mahawara a majalisa, Mr Netanyahu ya yi alwashin cewa: “Za mu dawo.”

Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya aika da sakon taya murna ga Mista Bennett, yana mai cewa a shirye yake ya yi aiki tare da shi.

Me ya sa hakan ta faru?

Mista Netanyahu ya yi wa’adin mulki sau biyar, na farko daga 1996 zuwa 1999, sannan daga 2009 zuwa 2021.

Ya kira sabon za?e a 2019 amma ya kasa yin nasarar kafa gwamnatin ha?aka. Daga baya aka sake yin wasu za?uka guda biyu, wa?anda dukkaninsu ba a kammala ba.

A za?e karo na uku ya haifar da gwamnatin ha?in kai inda Mista Netanyahu ya amince da tsarin kar?a kar?a ga jagoran adawa Benny Gants. Amma daga baya ?awancen ya rushe a watan Disamba, ya kai ga yin za?e kawo na hu?u.

Duk da jam’iyyar Likud ta Netanyahu ta samu kujeru 120 a majalisa, amma Netanyahu ya kasa kafa gwamnati, inda aikin ya koma ga Mista Lapid, wanda jam’iyyarsa ta zo na biyu da yawan ?uri’u.

Related posts

Leave a Comment