?asar Saudiyya Ta Tu?e Shugaban Limaman Masallacin Annabi


Rahotanni daga Birnin Makkah na ?asar Saudiyya na bayyana cewar Shugaban Masallatai biyu mafi daraja a Saudiyya Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya tu?e Daraktan da ke kula da limamai da ladanai a masallacin Manzon Allah a Madina.

An tu?e shi ne saboda samun jinkirin tayar da sallar Asuba bayan an kira Sallah na tsawon minti 45, kamar yadda Hukumomin da ke kula da Masallatan Makkah da Madina a Saudiyya, Haramain Sharifain suka sanar.

Social embed from twitter

Sanarwar da aka wallafa a Facebook ta ce shugaban Masallatan Sheikh Abdul Rahman Al Sudais ya bu?aci a samar da liman biyu a ko wace Sallar farilla.

“Liman na biyu zai kasance ne idan na farko ya makara,” in ji sanarwar.

Sabon matakin kuma ya shafi har da ladanai, inda sanarwar ta ce yanzu ladanai uku za a na?a a ko wace Sallar Farilla. ?aya zai kira Sallah, ?aya kuma ya tayar da I?ama, ?ayan kuma zai kasance idan an samu jinkirin fitowar ladanan.

Related posts

Leave a Comment