Gara A Kasheni Da A Biya Kudin Fansa – Amaryar El Rufa’i

Rahotanni daga Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna na bayyana cewar mai dakin gwamnan jihar Hajiya Asia El-Rufai, ta ce kada a biya kudin fansa domin karbo ta idan masu garkuwa suka sace ta gara a barta ta mutu a hannun su.

Matar gwamnan, wadda malama ce a Jami’ar Baze da ke Abuja ta ce a shirye ta ke ta mutu a hannun masu garkuwa da mutane idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar.

Ta yi wannan furucin ne yayin jawabin ta wurin taron zaman lafiya da tsaro da kungiyar Equal Access International (EAI) ta shirya a Kaduna.

ce ya zama dole yan Nijeriya su dawo da martabar kasar su da aka santa da zaman lafiya kuma mata na da muhimmin rawar da za su taka wurin cimma hakan.

“Dole sai munyi sadaukarwar kafin kawo karshen wannan lamarin kuma a shirye na ke in mutu a hannun masu garkuwa idan hakan zai kawo zaman lafiya a kasar nan.

“Idan har ka cigaba da biyan kudin fansa, kamar kana saka kalanzir ne a wuta, kana bawa yan bindiga, masu garkuwa kudin sayar makamai su cigaba da farautar ka. Bai dace mu biya kudin fansa ba. Wannan shine ra’ayi na.

“Na fada wannan a baya kuma zan sake nanatawa, Idan an sace ni, kada a biya kudin fansa. A maimakon hakan a yi min addu’a idan mutuwa ne, in cika da imani kuma idan za a sako ni kada a keta hakki na.

“Idan har za mu cigaba da ba su kudi, za su cigaba da zaluntar mutane, ba za su canja ba. A matsayin mu na yan kasa, dole mu ce tura ta kai bango. Ba za mu cigaba da basu kudinmu suna siyan miyagun kwayoyi da makamai ba suna kashe yaranmu. Idan ba mu dakatar da wannan ba, dukkan mu za mu hallaka. Har wanda ya kai musu kudin fansar.

Related posts

Leave a Comment