Rahotanni daga Birnin Maiduguri na Jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni su daina a kafafen sadarwa na zamani.
Ya yi rokon ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gasau ya fitar ranar Litinin.
Gwamnan ya yaba wa mutanen da ke tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika kwatanta “ayyukan da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da bambanci”.
“Duk da yake Ina matukar godiya bisa dukkan goyon baya da tallata ayyukana, a kwanakin nan, na samu sakonni, inda ake kwatanta ayyukan da muke yi a Borno da na wasu jihohi, a wasu lokutan ma ana zagi.
Gaskiya ba na jin dadi a duk lokacin da aka kwatanta ni da wani gwamna ta hanyar muzanta shi, musamman idan wadanda suke yin hakan suna cikin masu amfani da shafukan sada zumuntar da ke da alaka da mu”, in ji Gwamna Zulum.
