Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da jami’an tsaro da su yi aiki tsakanin su da Allah a za?en gwamna da za a yi a Jihar Edo a ranar Asabar ?in nan.
A cikin sa?on da ya aike wa da masu za?e da jam’iyyun siyasa da jami’an za?e da na tsaro, shugaban ya kuma yi garga?i kan abin da ya kira “tunanin siyasa irin na ko-a-mutu-ko-ai-rai.”
Mai taimaka wa shugaban ?asa kan al’amurran aikin jarida da ya?a labarai, Malam Garba Shehu, shi ne ya bada takardar shawarar da shugaban ya bayar a Abuja inda ya ruwaito Buhari ya na fa?in: “Na yi matu?ar sadaukar da kai na ga tabbatar da za?e cikin adalci, to amma tawa sadaukarwar ba ta wadatar ba ita ka?ai idan sauran masu ruwa da tsaki da ke wajen za?en ba su bi ?a’idoji ba.
”Ina so in ga an ?aga darajar dimokira?iyya a ?asar nan a kowane mataki, amma hakan ba zai samu ba idan su ‘yan siyasa sun hau matsayin a-mutu-ko-ai-rai don kawai su samu mulki ko ta halin ?a?a.
“Tunani irin na a-mutu-ko-ai-rai a siyasa barazana ne ga za?e cikin adalci da kwanciyar hankali domin su ‘yan siyasar sun fi maida hankali ne ga cin za?en maimakon su damu da samuwar sakamako cikin adalci wanda zai nuna bu?atar mutane masu za?e.”
Shugaban ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su da su bi doka da oda.
Ya shawarci jami’an za?e da na tsaro da “su kasance ‘yan baruwan mu don tabbatar da an yi za?e cikin kwanciyar hankali kuma cikin adalci. kuma su guji aikata duk wani abu da zai iya ?ata darajar za?en.”
Ya ce: ”Gudanar da za?e cikin kwanciyar hankali da adalci ya na daga cikin manyan abubuwan da na tsare a dimokira?iyyar mu, kuma ina so wannan sadaukarwar ta kasance ?aya daga cikin gadon da zan bar wa ‘yan baya idan na bar mulki.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) ta kammala dukkan shirye-shirye don gudanar da za?en gwamnan Jihar Edo a gobe Asabar.
Haka kuma ya ruwaito cewa ?an takarar jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, da na jam’iyyar PDP Godwin Obaseki, wa?anda su ne manyan ‘yan takarar da za su gwabza, sun riga sun rattaba hannu a kan wata takardar yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a za?en.
