Za?en 2023: INEC Za Ta Rijistar Masu Za?e

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce za ta fara aikin yin rijistan masu zade a farkon watanni uku na shekarar da ke tafe.

Shugaban hukumar na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya shaida hakan a ganawarsa da ‘yan jarida jimkadan bayan da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa kan INEC domin kare kasafin kudin hukumar na 2021.


Ya ce, za su shafe tsawon lokaci suna gudanar da rijistan masu zabe inda za a daina yin rijistar ana saura watanni shida gabanin babban zaben 2023.

Ya ce, “Hukumarmu tana da niyyar dawo da aikin rijistan zabe a farkon watanni uku na shekarar 2021. Da zarar muka dawo aikin, zai ci gaba da gudana har zuwa tsawon shekara daya da rabi, a takaice zai kai kusan saura watanni shida gabanin babban zaben 2023.”

Ya ce, idan sun dawo aikin ba wai za su ke yi mako-mako ko wata-wata ba ne, a’a aikin zai ke gudana a kowani lokaci ne amma za suke bin aikin ne da tattara komai ba wai na hanzari ba.
Shugaban hukumar ya ce yanzu haka INEC ta na fuskantar kesa-kesai a kotu na gabanin da bayan zaben 2019 har guda 1,700.

Ya ce, kesa-kesan suna gayar ci musu kudi amma duk da hakan suna kokarin bin matakan da doka ya tanadar na amsar kowace kara da aka makasu.

“Kowa idan ya tashi garzaya kotu sai ya hada da INEC, muna da kusan kesa-kesan kusan 1700 na gabani da bayan zaben 2019, muna ci gaba da amfani da dan kudaden da ke hannunmu,” A cewar shi.

A yayin da yake kare kasafin hukumar a gaban majalisar, Yakubu ya shaida wa ‘yan majalisar cewar hukumar na shirin fitar da naira biliyan N5.2 daga asusun INEC naira biliyan 10 domin karawa kan kasafin 2020.

Ya ce wannan biliyan 10 da suke zance a kai, yana daga cikin kudin da ke ajiye a asusun hukumar tun lokacin da aka kafa hukumar a 2010.

Ya ce bukatar hakan ya zama tilas ne lura da karancin kudin kasafin 2020 da suka samu kana da kuma matsalolin da suka fuskanto ciki kuwa har da wanda annobar Korona ta janyo da ya sanya hukumar ba ta samu cikakken kudin kasafin 2020 da aka tsara ba.

Kan ‘yan Nijeriya da ke kasar waje kuwa, ya ce akwai dokar da aka yi wanda aka tsara yadda su ma za su ke kada kuri’a a yayin da ake gabatar da zabe, a cewarsa da zarar dokar ya fara aiki za suke samun damar kada kuri’arsu daga kasashen da suke zaune.

Related posts

Leave a Comment