#EndSARS: Dalilan Buhari Na Yin Gum Akan Harbe-Harben Lekki -Fadar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai ce komai a kan harbe-harben da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki a ranar Talata ba a jawabin da yayi ga ‘yan Najeriya saboda baya son yayi riga Malam masallaci ne, domin ana kan gudanar da bincike, kamar yadda mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya bayyana.

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun nuna damuwarsu a kan rashin maganar shugaban kasan ko jaje ga jama’ar da suka rasa rayukansu. Sun kwatanta hakan da ganganci da kuma rashin nuna kulawa.

Amma kuma, mai bai wa shugaban kasar shawara na musamman a fannin yada labarai, Femi Adesina, wanda ya bayyana a shirin siyasarmu a yau a gidan talabijin na Channels, ya ce shugaban kasan bai samu cewa komai a kan harbin ba saboda ba a kammala bincike a kai ba.

“Hedkwatar tsaro ta fitar da takarda inda tace tana bincikar lamarin. Gwamnan jihar Legas ya kafa kwamitin bincike a kan abinda ya faru. “Toh don haka shugaban kasan bashi da ta cewa saboda zai zama tamkar riga Malam masallaci ne a kan binciken da ake yi. Bayan binciken ne zai yanke hukuncin magana a kai.”

Related posts

Leave a Comment