Zargina Da ?aukar Nauyin’Yan Bindiga Rashin Adalci Ne – Matawalle

Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya ya soki lamirin jam’iyyar APC mai mulki a kan zarginsa da daukar nauyin ta’addanci a arewa maso yammacin kasar nan. Inda APC ta fito ta yi mishi shagube da cewar yana da kyakkyawar alaka tsakanin shi da ‘yan Bindigar Arewa maso yammacin Najeriya.

Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam’iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta’addanci a arewa maso yamma.

Bayan jin hakan, gwamnan ya fitar da wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam’iyyar APC take yi.

Kamar yadda yace, abin ban mamaki shine yadda babu kunya ba tsaron Allah, za a zarge shi da bata lokacinsa da kokarinsa har na tsawon sa’o’i 100, wurin tabbatar da an sako yaran.

“Wannan al’amarin yayi shige da na wata takarda da gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya taba fitarwa kwanakin baya, lokacin da gwamna Matawalle ya dage wurin ceto yara 26 na karamar hukumar Faskari, na nan jihar Katsina.”

“Gwamna Matawalle ya dage wurin ganin ya kawo karshen ta’addanci a jiharsa. Kuma shugaba Buhari kullum cikin yaba masa yake yi. Yanzu haka jihar Zamfara tafi wasu makwabtanta zaman lafiya. Kuma ya yi alkawarin dagewa wurin ganin karshen ta’addanci a jiharsa.

“Gwamnan ya bukaci duk masu ruwa da tsaki, da su hada kai, kuma su yi kokarin kawo mafita a kan harkar tsaron da take addabar arewa.”

Related posts

Leave a Comment