Zanga-Zangar SARS: Babu Inda Na Yi Kiran Kaddamar Da Yaki – Yerima

Jagoran Kungiyar Matasan Arewa Alhaji Yerima Shettima ya nesanta kanshi da wani labarin ?anzon kurege da wasu Jaridun kudancin Najeriya suke ya?awa na cewar wai ya yi kiran ?addamar da ya?i ga jama’ar Kudu, muddin Zanga-zangar SARS ta yi nasarar kifar da Gwamnatin Shugaban ?asa Buhari.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da Kungiyar cigaban Matasan Arewan ta fitar ta hannun Babban Lauyan ?ungiyar Barista Abubakar Liman kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

Sanarwar ta kara da cewar wancan bayani da Jaridun suka ?auka, wani shiri ne na cin zarafi da ?o?arin shafa ba?in fenti ga Jagoran Matasan Arewa Yerima Shettima.

Ga duk wanda ya san Alhaji Yerima Shettima ya san shi a matsayin ?an kasa nagari mai tattalin ganin zaman lafiya a tsakanin jama’ar Najeriya, saboda haka wancan labari karya ce muraran aka shirya domin ?ata sunan shi.

Shugaban Matasan na Arewa bai ta?a shiryawa ko ?aukar nauyin yin wata zanga-zanga ba, shi ?an ?asa nagari ne wanda ya ke bi tsari da dokokin ?asa sau da ?afa.

Muna a matsayin ‘yan Arewa masu kishin Arewa, wa?anda ba za su lamunci dukkanin wani yunkuri na wulakanta yankin ba, amma a bisa ga tsari da doka ba hanyar tashin hankali ba.

Related posts

Leave a Comment