An kashe direban ministan ?wadagon Najeriya, Fetus Keyamo a zanga-zangar EndSars a ranar Laraba a Abuja.
A wani sakon Twitter da ya wallafa ministan ya ce, an kashe direbarsa Mr. Yohanna Shankuk, bayan ya ajiye mota sakamakon datse titi da masu zanga-zanga suka yi, sai ya yi kokarin takawa da ?afa zuwa ofishinsa.
Mutane da dama ne suka jikkata a zanga-zangar ta EndSars bayan wasu matasa dauke da makamai sun afkawa gungun mutanen da ke gangami akan titi.
Hotuna da bidiyo da aka ya?a a shafukan zumunta sun nuna yadda matasan suka ?ullo daga wani wuri daban ?auke da sanduna suna kai wa masu zanga-zangar hari.
?ungiyar kare ha??i ta Amnesty International ta yi zargin cewa wasu ne suka ?auki nauyin matasan domin tarwatsa zanga-zangar.
Kazalika, sun farfasa gilasan motoci kuma an ji wa wasu mummunan rauni.
Kusan mako guda kenan ana yin zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya domin neman yin gyara ga ayyukan ?an sanda a ?asar.
