Zan Iya Mutuwa Idan Ba A Sakeni Ba – Nnamdi Kanu

Madugun Tsagerun Inyamurai Nnamdi Kanu ya nemi gwamnatin Najeriya data taimaka ta bari a bada belin sa domin ya je Asibiti a duba lafiyar sa

Jagoran na masu kokarin kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu ya bayyana cewa yana cikin mawuyacin hali, don haka yake rokon gwamnatin Najeriya data taimaka ta bada belin sa domin ya je likitoci su duba lafiyar sa.

Haka su ma magoya bayan sa sun nemi kungiyar majalisar dinkin duniya da kuma ta kasashen Africa da su sanya baki don ganin an bada belin sa domin duba lafiyar sa.

Shin kuna goyon bayan gwamnati ta bada belin sa?

Related posts

Leave a Comment