Zan Gina Sabuwar Najeriya Idan Na Zama Shugaban Kasa – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ?an takarar Kujerar zama shugaban kasa a inuwar jam’iyya mai mulki ta APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace da ikon Allah ‘yan Najeriya ba zasu yi da nasani ba idan suka za?e shi shugaban kasa a 2023.

Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a wurin gangamin yakin neman za?ensa da ya gudana a Kaduna ranar jiya Talata.

Gangamin Kaduna somin ta?i ne na fara yakin neman zaben shugaban kasa na APC a shiyya mafi yawan kuri’u a Najeriya watau arewa maso yamma.

Da isarsa Kaduna ranar Litinin, Bola Tinubu ya zarce zuwa Birnin Gwari, ?aramar hukumar da ta’addancin ‘yan bindiga ya fi addaba a jihar inda ya ganewa idonsa yadda yankin da kuma shan Alwashin magance matsalar tsaro idan ya lashe zabe.

Da yake jawabi ga dandazon mutanen da suka fito tarbansa, tsohon gwamnan jihar Legas din yace idan aka za?e shi a 2023, zai kawar da ‘yan bindigan daji daga doron duniya. Haka zalika ya ?auki al?awarin fifita hanyoyin rage zaman kashe wando, samar da aiki mai gwabi ga matasa da kuma ha?aka noma ta hanyar kafa hukumar kasuwanci.

“Muna godiya ga Allah SWT da ya kawo mu nan kuma muna gode muku da kuka ci gaba da goyon bayan jam’iyyar mu, ba zaku yi dana sani ba insha Allahu.” “Duk wa?an nan masu ta da ?ayar baya, masu garkuwa, masu kashe-kashe da suka hana Kaduna zaman lafiya da arewacin Najeriya ina tabbatar muku zamu kawar da su Insha Allah.”

Related posts

Leave a Comment