Zan Dawo Da Martabar Aikin Jarida A Jihar Kaduna – Ahmed Maiyaki

IMG 20240413 WA0019

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewa shugaban kafafen yada labarai na Jihar (KSMC) Alhaji Ahmed Abdullahi Maiyaki, ya bayyana ?udiransa na dawo da martabar aikin jarida a jihar sannan da mayar da gidan Radiyo da Talabijin na Jihar Kaduna na zamani wanda zasu zama babu irinsu a nahiyar Afrika baki daya.

Alhaji Ahmed Maiyaki, ya ce gidan Radiyo da Talabijin na Jihar suna da dakin watsa shirye-shirye Wanda idan aka kammala gininshi zai zama babu irinsa a kasashen Afrika.

Maiyaki, ya bayyana haka ne yayin da dattawan Kungiyar ‘yan Jarida ta Jihar Kaduna suka kai masa ziyarar taya shi murnar samun mu?amin shugaban kafafen yada labarai na Jihar Kaduna, inda ya tabbatar da cewa zai Samar da tsare-tsare da zasu kara ?aga darajar gidan Radiyo da Talabijin na Jihar Kaduna Wanda zaiyi gogayya da na sauran kasashen duniya.

“Na Kai ziyarar gani da ido a sabon ginin da akeyi na dakin watsa shirye-shirye Wanda na zauna da ‘yan kwangila akan Yadda za’a kamalla aikin Wanda yanzu aikin ya kai Kashi 90 Cikin ?ari na kammaluwa Wanda idan aka kammala aikin zai zama duk nahiyar Afrika babu dakin watsa shirye-shirye kamar na KSMC”

“Za mu Samar da tsare-tsare na zamani da zasu kara bunkasa ci gaban gidan Radiyo da Talabijin na Jihar Kaduna saboda gida ne da zai samar da guraben aiki mai yawa ga ‘yan Jarida ”

Ahmed Maiyaki, wanda a makon da ya gabata ne gwamnan Jihar Kaduna ya na?a shi a matsayin sabon shugaban kafafen yaxa labarai na Jihar Kaduna KSMC.

Shugaban ya bukaci ‘yan Jarida da su ?ara jajircewa wajen ganin suna sauke hakkinsu na ‘yan Jarida maimakon su zama cima zaune.

Da yake nasa jawabin, jagoran ’yan Jaridan Alhaji Zakari Balare Ahmed, ya nuna gamsuwarsu dangane da kokarin gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani da baiwa Maiyaki shugaban kafafen yada labarai na Jihar inda yace babu shakka gwamnan yayi hangen nesa wajen baiwa kwararre jagorantar kafar yada labarai mallakar Jihar Kaduna.

Alhaji Zakari Balarebe Ahmed, yace matsayinsu na tsoffin ‘yan Jarida zasu tabbatar da sun bashi goyon bayan da ya kamata a kokarinsa na mayar da KSMC na zamani.

Related posts

Leave a Comment