Zan Cire Tallafin Mai Bai Da Amfani Ga Talaka – Tinubu

?an takarar shugabancin ?asa a jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya ci alwashin cire tallafin man fetur idan ya ci za?en shugaban ?asa da za a yi a watan gobe.

Tinubu ya ce zai cire tallafin man ne sabo da masu ku?i ne ke amfanar sa ba talakawan ?asa ba.

Da ya ke zantawa da gidan rediyon Freedom Radio ta wayar tarho, yayin da ya ke gudanar da ibadar Umurah a Saudiyya Tinubu ya ce tallafin man wata kafa ce ta asarar ku?a?e, inda ya ce idan ya hau mulki, zai karkatar da ku?a?en tallafin zuwa wasu hanyoyin da talakan Nijeriya zai amfana.

Ya ce abokan hamayyar APC duk sun razanar da irin shirin da jam’iyar ke yi na lashe za?en mai zuwa, inda ya nuna ya?inin cewa shi zai lashe za?en.

Related posts

Leave a Comment