A jawabin bankwana da Buhari ya gabatar ya amince da ?alubalen da gwamnatinsa ta fuskanta, musamman game da garkuwa da ?alibai da kuma matsalar tsaro.
Sai dai duk da haka shugaban ya nuna farin cikin cewa zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015 – lokacin da ya hau mulki.
“Yayin da nake shirin komawa Daura, Jihar Katsina, ina jin farin cikin cewa mun ?auki hanyar gyaran Najeriya ta hanyar ?aukar matakai masu muhimmanci,” a cewarsa.
“Ina da ?warin gwiwar zan bar mulki a 2023 yayin da Najeriya ta inganta fiye da yadda na same ta a 2015.”
A yau Litinin Buhari zai mi?a mulki ga Bola Ahmed Tinubu, wanda ya lashe za?en shugaban ?asa a ?ar?ashin jam’iyyar APC mai mulki, bayan shekara takwas yana jagoranci.
