Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, ya ce an kammala tattauna wa da babban ?an shugaban ‘yan bindigan da aka kashe, Buharin Daji, wanda ya cigaba da jagorar ‘yan Bindiga tun bayan kisan da aka yi wa mahaifinsa.
Gwamnan ya kara da cewa ?an Buharin Daji, mahaifiyarsa da wani babban jagoran ‘yan bindiga a Zamfara za su ajiye makamai, su rungumi sulhu da zaman lafiya da sauran jama’ar Jihar.
Gwamnan na Zamfara ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya zauna da tawagar shehin malamin nan na Kaduna, Dr. Ahmad Abubakar Gumi, wanda ya sadaukar da rayuwarshi wajen fuskantar ‘yan Bindiga.
Matawalle ya ce matakin da ‘yan bindigan su ke shirin dauka na ajiye makaman yaki zai yi sanadiyyar samar da zaman lafiya a jihar Zamfara, dama sauran Jihohin da ke makwabtaka da ita.
Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya ce ba don jajircewarsa ba, da ya yi watsi da sulhun da aka ayi da ‘yan bindiga, saboda akasin ra’ayin da wasu su ke da shi.
“Ana ta matsa mani lamba daga wurare da-dama saboda na yi sulhu da ‘yan bindiga, wasu sun ce ina cikinsu, wasu sun ce ina ba su kariya.” Inji Gwamnan.
Mun ga tasirin kwarai na wannan yarjejeniyar (sulhu). Kasuwannin kauyuka su na dawowa. Mun ceto mutanen da aka tsare ba tare da harbin ‘dan kowa ba.”
“Idan mun san za a iya kawo karshen rikicin da karfin bindiga, da ba zamu yi sulhu ba. Za kuma mu cigaba da yin haka, duk da abin da mutane za su ce.”
Anashi ?angaren Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya bayyana ainihin abin da ya jawo har ta’adin ‘yan bindiga ya yi kamari sosai a yankin Arewa maso yamma.
Malamin ya yi magana bayan ya hadu da ‘Yan bindiga a Zamfara, ya ce ta’addanci ne ba tsageranci ba. Ahmad Gumi ya bayyana cewa rashin kula ne ya jawo wadannan mutane su ka zama gawurtattun ‘yan ta’adda, ya bada shawara ayi sulhu da su.
