Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin jihar Zamfara na bayyana cewar Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar 17 ga watan Afrilu don sauraron karar neman tsige Gwamna Bello Matawalle na Jihar saboda ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
A cikin karar, jam’iyyar PDP ta bukaci kotun ta ayyana tsigaggen mataimakin gwamna Mahdi Aliyu Gusau a matsayin hallastaccen gwamnan Jihar Zamfara.
PDPn ta kuma bukaci kotun ta kori yan majalisar tarayya da na jiha kimanin 37 da suka koma jam’iyyar APC, ba tare da ?ata lokaci ba.
