Zamfara: Matashin Dan Ta’adda Mai ‘Yanmata Ya Shiga Hannu

Rundunar ?an Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wani ?asurgumin ?an fashin daji, Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-?anmata a jihar.

Rundunar ta ce Mai-?anmata, ?an shekara 20 kacal da haihuwa, ya ?ware wajen garkuwa da mutane, fashin daji, satar shanu da sauran manyan laifuka a yankin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara.

Kwamishinan ?an Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba N. Elkanah ne ya baiyana haka a taron manema labarai yayin da rundunar ta yi holon ?an ta’addan a juya Laraba.

A cewar Kwamishinan, ” a ranar 28 ga Disamba da misalin ?arfe 5 na yamma, yayin da su ke wani sintiri na sirri bayan sun samu bayanan sirri, sun cafke wani ?asurgumin ?an fashin daji mai suna Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-?anmata ?an ?auyen Mayasa a ?aramar Hukumar Zurmi.

Ya ?ara da cewa Mai-?anmata ya shiga komar ?an sanadan ne lokacin yana shirin sanya shinge ya tsare bayin Allah domin ya yi garkuwa da su a daidai wani ?auye mai suna Koliya.

Elkanah ya ?ara da cewa da a ?angaren Turji Mai-?anmata ya ke, inda yanzu ya koma sansanin wani ?asurgumin ?an fashin daji mai suna Kachalla Sani Black.

Ya ce an samu bindiga samfurin AK-47, sai kwanson harsashi 2, sai harsashi 3 da kuma babur guda 1.

Ya ce a na nan a na yi masa tambayoyi inda da ga nan za a ki shi kotu.

Related posts

Leave a Comment