Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Haukumar tsaro (NSCDC), ranar Laraba, ta sanar da kame wasu tsagerun yan bindiga guda hu?u akan iyakar Jihar Zamfara da jihar Sokoto.
An ruwaito cewa wa?anda ake zargin ‘ya’yan manyan ?ungiyoyin yan bindiga ne da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara, Kaduna da Jihar Katsina.
An yi nasarar damke mutanen ne bisa zargin hannu a garkuwa da manyan mutane, fashi da makami, satar dabbobi da kuma kashe mutane a wasu yankunan wa?annan jihohi.
Kwamandan jami’an NSCDC reshen jihar Sokoto, Mohammed Saleh-Dada, yace wasu daga cikin mutanen da aka damke yan leken asirin yan bindiga ne. A cewar kwamandan hukumarsu ta gayyaci wani babban mutum da ake zargin yana da ala?a da ?aya daga cikin mutanen da aka kame.
“Mun gayyaci wani sanannen mutum a yankin karamar hukumar Dange/Shuni, jihar Sokoto, bisa zargin yana da wata ala?a da mutum daya da ake zargi.”
