Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewa Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle ya ce gwamnatin jihar ta gano sunayen likitocin bogi kimanin 199 wa?anda ake biyan albashi a jihar.
Gwamna matawalle na wannan jawabi ne ga taron manema labarai a shalkwatar ?aramar hukumar Maradun da ke jihar.
A cewar gwamnan yayin da gwamnatin jihar ke biyan likitoci 280 albashi a jihar a duk wata, ta gano cewa likitoci 81 ne kawai ke aiki a jihar.
Gwamnan ya ?ara da cewa tuni ya zanta da ?ungiyar kwadago ta ?asa domin gano wa?anan, likitoci 199 da suka ?washe tsawon lokaci suna kar?ar albashi alhalin ba sa yi wa gwamnatin jihar aiki.
Da kuma gano wa?anda ke da hannu a wannan cuwa-cuwa.
Matawalle ya ce an gano wa?annan sunaye ne sakamakon aikin tantance ma’aikata da gwamnatin jihar ke gudanarwa ?ar?ashin ofishin shugaban ma’aikata na jihar.
