Kotun majistiret na biyu a jahar Adamawa ta daure wani matashi daurin shekaru biyu a gidan yari tare da zabin biyan dubu hamsin ko kum daurin watanni shida ba tare da zabi ba.
Kotun kakashin mai Shari’a Japhet Basani an yanke hukuncin daure matashin mai suna Ali Yakubu Numan ne biyo bayan samunsa da laifin ciwa gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fntiri mutunci.
Shidai Ali Numan tun a ranakun 11, 12, 13,17.20.da kuma 29 na watan bakwai na shekara 2021 ne dai ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shine Baban barayi kuma ya saci kudade masu dama da dai sauransu.
Tunda farko dai lauyoyi masu gabatar da kara wato A M Iliyasu tare da M A Adamu sun gabatarwa kotun cikakkun shaidu wanda hakan yasa aka samu Ali Yakubu Numan da lafin zagin gwamna jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri.
Shima anashi bangaren lauyan wanda ake kara R N Agav ya nemi da ayiwa wanda ake karan adalci tare da tausayawa kasancewa.
