Zaben Najeriya: Hukumar Zabe Ta Yi Rawar Gani – Kungiyoyin Sa Ido

A daidai lokacin da ake cigaba da dakon zuwan sakamakon za?e na shugaban ?asa da ‘yan Majalisun ?asa da aka gudanar a Najeriya ranar Asabar.

Shugaban gidauniyar MCArthur, Dakta Kole Shettima ya ce sun yaba da yadda hukumar za?en Najeriya ta shirya za?en ?asar.

To sai dai ya ce duk da haka akwai matsaloli kamar na mutanen da ba su san inda za su yi za?e ba sakamakon sauya wuraren za?e da aka yi.

‘’Sannan kuma mun lura cewa ba duka jam’iyyun ba ne ke da wakilansu a rumfunan za?en’’, in ji Dakta Kole.

Sannan kuma ya ce akwai matsalar rashin bu?e rumfunan za?e a kan lokaci,

Ya ?ara da cewa akwai matsalar rashin aikin na’urar BVAS kamar yadda ya kamata a wasu wurrare.

Ya kuma yaba da yadda matasa suka nuna jajircewa a za?en saboda suna ganin ko ma me a ke ciki za su jira, ‘’amma kuma duk da haka mun samu labarin cewa wasu sun gaji, sun kuma bar rumfunan za?en’’, in ji shi.

Dakta Kole Shettima ya ce ya kamata a bai wa mutanen da ba su yi za?e ba damar sake yin za?e ko a gobe ne, ko ranar Litinin kasancewar ma’aikatan za?en ba su zo da wuri ba.

Dakta Kole Shettima ya kuma koka kan rashin bai wa mata dama a za?en Najeriya.

Sannan ya kuma ce ya yaba da yadda INEC ke ?o?ari wajen inganta harkokin za?en ?asar, ba kamar shekarun baya ba.

Related posts

Leave a Comment