Zaben 2023: Za Mu Ba INEC Hadin Kai – Gwamnan Babban Banki

Gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele ya tabbatar wa hukumar za?en Najeriya INEC cewa babban bankin ba zai yi wani abu da zai kawo cikas ga za?en 2023.

An ruwaito cewa Mista Emefiele yana bayyana hakan bayan ya kar?i ba?uncin shugaban na INEC Mahmood Yakubu.

Shugaban na INEC tun da farko ya shaida wa shugaban CBN irin tasirin da sauyin ku?in Najeriya zai yi ga za?en.

Shugaban na INEC ya bu?aci babban bankin da ya sauya wasu tsare-tsare musamman ma kan batun ?ayyade kudin da za a iya cirewa a duk rana domin a samu ku?in da za a yi amfani da su a wasu ayyuka wa?anda ba za a samu damar tura su ta intanet ba.

Ya bayyana cewa akwai wasu ayyuka musamman masu motocin haya wa?anda dole da ku?i lakadan za a biya su, kuma ya bayyana cewa saboda da?ewa a wannan aikin na za?e sun ga abubuwa iri-iri inda ya ce ana samun bu?atu na gaggawa a ranakun za?e inda hukumar ke bu?atar amfani da ku?i.

Related posts

Leave a Comment