Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya Aisha Buhari ta bukaci matan Najeriya da su hada kai domin tunkarar babban zaben dake tafe na shekarar 2023.
Uwargidan shugaban kasar ta ce hakan zai tabbatar da sun yi tasiri mai karfi a harkokin zabe.
Ta kuma bukaci jam’iyyar APC Mai Mulki ta kasa, da ta dauki sabbin dabaru don tabbatar da cewa mata da yawa sun shiga cikin manyan Masu ruwa da tsaki a harkokin mulki.
Uwargidan Shugaban kasar ta bayyana hakanne a ranar Litinin lokacin da ta karbi bakuncin mataimakiyar shugaban kasar Laberiya Jewel Howard-Taylor.
Mataimakiyar ta zo Najeriya ne domin taron mata na Kasa, don kawo ci gaban a jam’iyyar APC na kasa.
A’isha ta bukaci masu ruwa da tsaki da su tallafa wa jinsi domin cimma bukatarsu ta kara shiga harkokin siyasa.
“Mata na bukatar a karfafa musu gwiwa su kara shiga harkokin siyasa kuma kasar na bukatar shigar mu.
“Ya zama dole mu sanya ido kan yadda za mu yi aiki tare don hada kan mata a yakin neman zabe mai zuwa gabanin zaben 2023.”
Ta ce kasancewar Howard-Taylor da kalamanta za su kara kwarin gwiwar mata da ke halartar taron.
Aisha ta kara da cewa “Na gamsu cewa tarihinki a matsayinki na tsohuwar uwargidan shugaban kasar Laberiya kuma kwararre kan harkokin siyasa zai kara manakarfin guiwa a wannan taron.”
A nata jawabin, Howard-Taylor ta yi kira da a kara Samar da kayan aiki don ilmantar da mata, karfafawa, kariya da kuma kula da lafiyar mata da yara.
