Za Mu Koyar Da Matasa Dubu 30,000 Ilimin Fasahar Zamani – Pantami

Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace za’a horad da karin matasan Najeriya sama da 30,000 ilimin fasahar zamani.

An ruwaito cewa wannan na ?aya daga cikin amfanar da yan Najeriya za su yi da hadin guiwar ma’aikatar sadarwa da kamfanin Huawei Technologies Nigeria.

Ministan ya yi wannan jawabi ne yayin rattaba hannu a yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) tsakanin ?angarorin biyu, da nufin ?ara inganta ilimin zamani (Digital Literacy) ga yan Najeriya.

Kazalika kamfanin ya yi amfani da taron wajen mika kyaututtuka ga wa?anda suka samu nasara a zango na karshe a gasar Huawei.

“Yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta sa wa hannu ta ma’aikatar sadarwa, a ?aya hannun kuma kamfanin Huawei Nigeria, zai maida hankali ne wajen kara inganta kwarewar yan Najeriya.”

“Musamman saboda yadda duniya ke canza wa a yanzu, akwai bukatar dalibai su samu kwarewar fasaha da za su iya yin abu a aikace . “Shiyasa mukai tunanin samar da MoU domin ganin, a ?angaren kokarin da kamfanin Huawei ke yi, sun tallafa wa dalibai a fa?in ?asar nan.”

Related posts

Leave a Comment