Ministan Lafiya a Najeriya, Dr. Osagie Ehanire, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta yi dukkanin abin da za ta iya domin cirewa likitoci sha’awar barin kasar zuwa kasashen waje aiki.
Ya ce gwamnatin za ta yi hakan ne ta hanyar samar da abubuwan da suka dace domin cirewa likitocin sha’awar kauracewa kasar.
Ehanire ya sha alwashin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake duba aikin ginin wata sabuwar cibiyar kula da cutar daji a babban asibitin kasa da ke Abuja.
“Na ji irin kalubalen da ake fuskanta na barin kasar nan da likitoci ke yi, kuma muna da tsare-tsaren samar da karin kudade ga asibitocin Najeriya domin hana su yin kaura zuwa waje,” in ji Ministan.
Ministan ya kuma jinjinawa asibitin bisa kwazon da ta yi a lokacin kololuwar cutar COVID-19 a kasar, yana mai alkawarin gwamnati za ta yi iya kokarin ta domin tabbatar da ganin likitoci sun ma fi son su yi aiki a gida a maimakon kasashen waje.
A yayin da yake ci gaba da jawabi, Ministan ya shawarci hukumomin asibitin da su rinka amfani da kudade ta hanyar da ta dace, su kuma baiwa cibiyar cikakkiyar kulawa idan aka kammala ta, sannan su nemo wasu hanyoyin samun kudade.
Da yake nasa jawabin, shugaban asibitin, Dr. Jaf Momoh, ya bayyana cewa babban asibitin kasar ya bullo da wasu hanyoyin karfafawa likitoci gwiwar zama su yi aiki a cikin Najeriya.
A tsakanin hana shuwagabanni fita kasashen ketare neman lafiya da kuma hana likitoci zuwa aiki kasashen ketare wanne ne zai kawo cigaba a fannin kowon lafiya?
