Za Mu Fallasa Asirin ‘Yan Bindigar Dake Cikinmu – Miyyeti Allah

?ungiyar Miyetti Allah reshen Taraba ce ta ?auki wannan matakin tsakanin mambobinta da suka ?unshi shugabanin Fulani makiyaya da ardo-ardo a fadar Sarkin Muri Alhaji Abbas Tafida.

Shugaban ?ungiyar Miyetti Allah na jihar Taraba Alhaji Sahabi Mahmud Tukur ya shaida wa BBC cewa wa’adin wata biyar ?ungiyar ta ba kanta domin kakka?e ?ata-garin da ke ?ata sunan Fulani makiyaya.

“Idan akwai ?atattu cikinmu za mu kira su mu tattauna da su mu nuna musu gaskiya idan kuma suka ?i za mu mi?a su ga hukuma.”

“Idan an ce ba mu da kyau, to za mu duba domin mu gano su don mu gyara wankanmu ko da kuwa ?a?anmu ne,” in ji shi.

Ya ?ara da cewa wannan aikin da suka yi al?awali ya zama wajibi domin wanke sunan Fulani daga ?ata sunan da ake masu na fashi da makami da satar mutane.

Shugaban na Miyetti Allah a Taraba ya yi i?irarin cewa ba Fulani ba ne kawai ke aikata laifin fashi da makami da satar mutane ba – “amma an fi fakewa da Fulani shi ya sa muka yanke shawarar shiga cikinmu mu fito da duk wani mai aikata laifi domin wanke zargin da ake muna.”

Miyetti Allah ta ce za yi amfani da ?an banganta a sassan Taraba da ke kula da rumfunan Fulani domin tantance ?ata-gari daga cikinta domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Sai dai ?ungiyar makiyayan ta bayyana damuwa kan yadda jami’an tsaro ke kama ?a?an Fulani da ba su ji ba su gani ba.

Alhaji Sahabi Mahmud Tukur ya bu?aci sarkin Muri ya gabatar da korafinsu ga gwamna Darius Ishaku kan yadda ake kama Fulani ba tare da tabbatar da zargin da ake masu ba inda ya bu?aci gwamnati ta saki wadanda aka tabbatar da ba su da laifi.

A lokacin bikin Babbar Sallah ne Sarkin Muri, Abbas Tafida, ya bai wa Fulani makiyaya wa’adin kwanaki 30 na su bar dazukan jihar ko kuma su daina garkuwa da mutane.

Kalaman nasa sun jawo ce-ce-ku-ce tsakanin al’umma da makiyaya.

Related posts

Leave a Comment