Sakataren Ri?o na ?asa na Jam’iyyar APC, John Akpanudoedehe, ya bayyana cewa za sha dibirin labarai kenan idan tsohon Shugaban ?asa, Goodluck Jonathan ya sauya she?a, ya koma jam’iyyar PDP a za?en 2023.
Da ya ke bayani a gidan Talabijin na Channels, Akpanudoedehe ya ce ba shi da wani cikakken labarin shirin Jonathan zai koma PDP.
“Amma dai idan ya dawo cikin mu a APC, to za a ba shi mu?ami na musamman, daidai da manyan iyayen jam’iyya da su ka kafa ta. Za a ba shi damar fitowa takarar shugabanci a za?en 2023 kamar yadda za a bai wa kowa dama.”
An da?e ana ra?e-ra?in cewa Jonathan zai koma APC, duk kuwa da shi kan sa ya ce ya daina shiga lamarin siyasa, zai zauna ne ya maida hankali wajen ayyukan jin?ai wa?anda ya ke yi a cikin al’umma, musamman a Afrika.
A ranar Laraba ?in nan ce kuma Kakakin Ya?a Labarai na Jonathan, Ikechukwu Eze ya bayyana cewa labarin da ake ya?awa wai Jonathan zai koma APC, na bogi ne, ba gaskiya ba ce.
Duk da cewa Shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa a 2023, har yau APC mai mulki ba ta tsaida ko nuna ?an takarar ta shugaban ?asa ba.
Sai dai ‘yar manuniya na nuni da cewa mulki ko kuma a kudu za a bayar da takarar shugaban ?asa a ?ar?ashin APC ?in. A kudun ma an fi han?oron a bai wa yankin Kudu maso Yamma.
Jonathan dai zango ?aya ya yi, inda Buhari ya kayar da shi a ?o?arin na ?arasa zangon sa na biyu.
Bayan an kayar da shi, Jonathan ya sha yabo a Najeriya, Afrika da duniya baki ?aya, saboda bai nuna fifikon son zama kan kujerar sa ko a mutu ko a yi rai ba.
Daga baya Gwamnatin Buhari ta jawo shi a jiki, aka ri?a tura shi ?asashen da ake husumar shugabanci domin sasantawa. Kuma ya na wakiltar Najeriya a za?uka a ?asashen da ake so dimokra?iyya ta ?ore a Afrika.
Har yau ita ma PDP ba ta nuna ?an takarar ta a za?en shugaban ?asa na 2023 ba.
