Za A Wadata ‘Yan Sanda Da Kayan Aiki Domin Fuskantar Zaben 2023 – Shugaban ‘Yan Sanda

Sifeta janar na ?an sandan Najeriya Usman Alkali ya bayar da umurnin bai wa ?an sandan ?asar sabbin kayan sawa da na aiki domin su samu damar gudanar da aikin za?en shekara ta 2023 yadda ya kamata.

Baya ga sabbi kayan sarki, sauran kayan da za a bai wa jami’an ?an sandan sun ha?a da na korar masu zanga-zanga, da rigar surke, da hular kwano, da haya?i mai sa hawaye da sauran su.

Sifeta janar na ?an sandan ya ce wa?annan kaya za su taimaka wa ?an sandan wajen gudanar da ayyukansu gabanin babban za?en ?asar na 2023, da lokacin za?en da kuma bayansa.

Wannan umurni na zuwa ne bayan kayan da aka sayo na ?an sanda domin inganta walwalar jami’an hukumar, yayin da ake ci gaba da ganin yadda za a tabbatar da ?warewa wurin aiki.

Sai dai IGP Usman Alkali ya bu?aci jami’an hukumar da su kare martabar aikinsu da kuma kare hakkin al’umma.

Related posts

Leave a Comment