Za A Maye Gurbin Lambobin BVN Da NIN – Pantami

Ministan Sadarwa da sabon tsarin gina tattalin arziki Dakta Isa Ali Pantami, ya ce gwamnatin tarayya tana kan hanyar maye gurbin matsayin BVN da NIN.

BVN lambobi ne na tantancewa da bankuna suke ba abokanan harkar su.

Tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Sanusi Lamido, ne ya bullo da tsarin BVN domin tsaftace harkokin bankuna da kuma magance badakala da cin hanci.

Hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa, NIMC, ce ke bayar da lambobin tantancewa na NIN ga kowanne dan kasa da ya yi rijista da gwamnati.

Da yake jawabi ranar Litinin yayin da ya kai ziyara domin ganin aikin rijistar dan kasa a Abuja, Pantami ya ce za’a koma aiki da NIN a bankuna, sabanin amfani da BVN.

“Tuni na ja hankalin majalisar koli ta bunkasa tattalin arzikin kasa da gwamnan babban bankin kasa (CBN) akan bukatar yin hakan.

“Na bashi hujjar cewa NIN ta fi BVN muhimmanci saboda ita ta kasa ce ba wani bangare daya kadai ba.

“An riga an kirkiri doka akan NIN, ita kuwa BVN tsarin banki ne kawai, wanda bashi da tasiri ko karfi fiye da dokar kasa,” a cewarsa.

Pantami ya kara da cewa komawa amfani da NIN zai tabbatar da samun karuwar tsaro da tsare sirrin bayanan ‘yan kasa.

Related posts

Leave a Comment