Ministan ?wadagon Nijeriya Chris Ngige ne ya sheda hakan ga manema Labarai
Ya fara da cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin tarayya za ta bayyana ?arin albashi ga ma’aikatan gwamnati a ?asar domin rage ra?adin tashin farashin kayyaki da ake fuskanta a ?asar a halin yanzu.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai jim ka?an bayan ya yi wata ganawar sirri da shugaban ?asar Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Aso Villa A Birnin tarayya Abuja.
Ya ce kwamiti kan albashi da shugaban ?asar ya kafa na sake duba batun albashin ma’aikata a ?asar, kuma ana sa ran zai zo da bu?atar ?arin albashin a shekara mai kamawa ga Daukacin Maaikatan kasar lura da hauhawan farashi da ake fuskanta ga kuma Albashi na Tsaye gu guda.
Da aka tambaye shi ko sun tattauna wannan batu tare da shugaba Buhari, sai ministan ya ce ”?warai kuwa, wannan shi ne abin da nake fa?a cewa kwamitin albashi da shugaban ?asar ya kafa na aiki kafa?a-da-kafa?a da hukumar albashin ma’aikata ta ?asar”.
“Dan haka yayin da muka shiga sabuwar shekara gwamnatin tarayya za ta ayyana batun ?arin albashin”, in ji ministan.
