Za A Kafa Dokar Dauri Da Tarar Masu Dibar Dukiyar Kasa Suna Fita Waje Neman Magani

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ‘Yan majalisar dokokin tarayya na shirin kafa wata dokar da ta tanadi tarar miliyoyin Naira ko kuma daurin shekaru bakwai, ga masu laifin kwashe kudin gwamnati da sunan neman lafiya a kasashen waje.

An ?iyasta kusan dalar Amurka miliyan 500 ne manyan jami’ai da sauran ‘yan boko ke batarwa a shekara da nufin zuwa kasashen Turai, domin neman magani na cutuka iri-iri.

Kuma mafi yawan masu ziyarar na zaman manyan jami’an gwamnati a matakai dabam-dabam, abun kuma da majalisar tarayya ke neman sauyawa tare da  kokarin kafa wata dokar da ta tanadi daurin shekaru bakwai ko kuma tarar Naira miliyan 500 kan kowane jami’in gwamnatin da ya kwashi kudin gwamnati domin neman lafiyar.

Sabuwar dokar da ta haura karatu na biyu a zauren majalisar wakilan kasar dai, na da burin ingantar  tsarin lafiya a kasar da asibitoci ke korafin rashin kayan aiki da magani. Dokar dai ta ce ba wani jami’in gwamnati da zai kara fita wajen kasar domin duba lafiya ko kuma asibiti, har sai ya samu amincewar wata hukuma ta musamman a karkashin jagorancin ministan lafiya a matakin tarayya ko kuma kwamishinan lafiya a jihohi.

Related posts

Leave a Comment