Za A Iya Ha?a Lambobin Waya 7 Da Katin ?an ?asa Guda – Pantami

Ministan Sadarwa da tattalin arzki na digital Sheikh Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa za a iya hada layukan waya dabam-dabam har bakwai da lambar katin zama dan kasa guda daya.

Sheikh Pantami ya fadi haka ne a lokacin da ya amsa tambayoyi a wani shirin gidan talbijin din Channels dake Abuja.

”Mun kirkiro manhaja da za ka iya hada layuka bakwai da lambarka na katin zama dan kasa nan take cikin sauki. Mun yi haka ne domin a samu saukin hada layukan ba tare da an wahala ba.

Hukumar NIN ta gargadi kowani dan kasa ya je yayi rajistan kansa domin samin lambar zama dan kasa kuma ya hada layin sa da lambar kafin 9 ga Faburairu.

Related posts

Leave a Comment