Ba Na Goyon Bayan Biyan Kudin Fansa Ga ‘Yan Bindiga – Dr Gumi

IMG 20240315 WA0034~2

Babban malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya yi magana kan kuskuren da gwamnatin tarayya ke yi wajen ceto ?alibai 287 da malamansu da aka sace a jihar Kaduna.

SheikhGumi ya nuna cewa kuskure ne amfani da ?arfi wajen ganin an ceto ?aliban a hannun ?an bindiga.

Da yake magana a wani shirin gidan talabijin na Arise tv, a ranar Alhamis a Abuja, Gumi ya ce ya kamata gwamnati ta matsa kusa da ?an bindigan ta yi nazari a kansu domin samar musu da ingantacciyar rayuwa.

A cewarsa, amfani da ?arfi da gwamnati ke yi yanzu ya mayar da ?an bindigan sun zama dodanni. A kalamansa: “Wa?annan ?an bindigan suna ?ara ta’azzara. A baya basu yin haka. ?an ?ananan marasa rauni suke farmaka, ?ara ?arfinsu za mu danganta shi da ?arfin da ake amfani da shi a kansu.

“Yanzu muna ya?ar ?an bindiga. Ba a san sunansu ba. Ba za a iya fa?a da wanda ba a sani ba. Mun ce a shiga, a gano su, mu tsara su, mu san su waye da kuma inda suke.

“Duk wa?annan bayanan sirri kusan babu su. Hanyar amfani da ?arfin da ake bi ita ce ke ?ara tar?ar?ar da lamarin. “Yanzu haka suna garkuwa da yara tare da barazanar kisa, wanda a da ba su yi ba. Don haka, ina tunani abin da ya kamata shi ne a koma a sake lale a daina amfani da ?arfi.

Ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga yan bindigar akan yadda za a kawo ?arshen matsalar, ya ce kamata ya yi gwamnati ta tsara wani shiri kamar irin shirin yin afuwa ga tsagerun Neja-Delta da aka yi a baya.

A kalamansa: “Ana bu?atar shiri kamar na Neja-Delta, shirin da zai fitar da su daga dazuzzuka, ilimantar da su, ba su kiwon lafiya, ba su ingantacciyar rayuwa. “A haka ake sanya wa mutane su bar tashin hankali da fitina.

Related posts

Leave a Comment